1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kashe sojoji 12 a kudu da birnin Hodeida

Mohammad Nasiru Awal MNA
June 15, 2018

Gommai na mayaka aka kashe tun lokacin da aka fara kai farmakin a ranar Laraba. Majalisar Dinkin Duniya ta nuna damuwa da hali da ake ciki.

https://p.dw.com/p/2zdNS
Jemen Hodeida Kämpfer
Hoto: picture-alliance/AP Photo/N. El-Mofty

Wani hari da 'yan tawayen kasar Yemen suka kai a kudu da birnin Hodeida mai tashar jirgin ruwa ya halaka sojoji 12. Majiyoyin soja da na jami'an kiwon lafiya sun ce 'yan tawayen sun kaddamar da harin ne kan wata hanya da ke a gabar teku daga tashoshin jiragen ruwa na Khokha da Mokha da ke hannun gwamnati, wanda dakarun da ke karkashin jagorancin Saudiyya suka bi ta kai suka kutsa cikin Hodeida a farkon wannan mako.

Harin da aka kai a wani yanki mai tazarar kilomita 80 kudu da Hodeida na zama wani yunkuri na karkata hankula daga ainihin filin daga da ke kewayen filin jirgin saman birnin da ba a amfani da shi.

Gommai na mayaka aka kashe tun lokacin da aka fara kai farmakin a ranar Laraba. Majalisar Dinkin Duniya nuna damuwa game da muhimman kayan agaji da ke bi ta tashar jirgin ruwan wannan yanki.

Tun a shekarar 2014 birnin na Hodeida ke hannun 'yan tawaye. Kwace birnin zai zama nasara mafi girma ga kawancen da ke yakar 'yan tawaye.

A ranar Alhamis jagoran 'yan tawaye Abdel Malek Al-Huthi ya yi kira ga mayakansa da su kara zage dantse su kuma jure da kowane hari daga abin da ya kira 'yan katsalanda.