1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan tawayen Siriya sun kauracewa birnin Homs

March 2, 2012

A karon farko 'yan tawaye sun tsere daga birnin Homs, bayan da dakarun gwanati suka dauki kwanaki da dama suna musu luguden wuta

https://p.dw.com/p/14CvD
Members of the Free Syrian Army are seen deployed in al-Bayada district in Homs, February 28, 2012. Most Syrian rebels pulled out of the besieged Baba Amro district of Homs on Thursday after a 26-day siege by President Bashar al-Assad's forces, activists in contact with the fighters said. Picture taken February 28, 2012. REUTERS/Stringer (SYRIA - Tags: POLITICS CIVIL UNREST CONFLICT)
Dakarun 'yan tawaye a HomsHoto: Reuters

Bayan da dakarun gwamnatin Siriya suka sha karfin su, 'yan tawayen kasar sun gudu daga makarfafar ta su ta birnin Homs, sakamakon kwanaki 26 da dakarun suka shafe suna luguden wuta a birnin da a yanzu haka ke zaman wata alama ta nuna adawa da gwamnatin Bashar al Assad. A dalilin haka ne ma a wannan juma'ar kungiyar agaji ta kasa da kasa ta Red Crescent ta dauki wannan a matsayin wata dama na shigar da kayyayaki zuwa Baba Amr. 'yan tawaye masu dauke da makamai da sojojin da suka sauya sheka ne suka jagoranci wannan bore wanda ya fara a matsayin wata zanga-zanga ta lumana, bayan kadawar guguwar sauyi a kasashen larabawa.

To sai dai abun ya ta'azara, bayan da dakarun gwamnati suka fara murkushe su. Majalisar Dinkin Duniya ta ce kimanin mutane 7500 suka hallaka tun bayan da aka fara zanga-zangar a watan Maris din bara, kuma Majalisar ta yi kira ga mahukuntan Siriyan da su baiwa shugaban hukumar kula da yan gudun hijirarta wato Valerie Amos damar shiga biranen da suka fi fama da rikicin. kasashen Rasha da China su sanya hannu kan sanarwar da ta tanadi yin hakan, bayan da mahukuntan siriyan suka hana shugabar hukumar shiga kasar.

Mawallafiya: Pinado Abdu-Waba
Edita: Mohammad Nasiru Awal