1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan tawayen Siriya sun kai hari a Lebanon

August 2, 2014

'Yan tawayen sun ce sun ɗau wannan matakin ne don kuɓutar da 'yan uwansu da ke cikin hannun hukumomin Lebanon ɗin.

https://p.dw.com/p/1Cnx2
Libanon Stadt Arsal an der Grenze zu Syrien
Hoto: picture-alliance/AP

'Yan tawayen Siriya da ke fafutukar kawar da gwamnatin Shugaba Bashar al-Assad sun afkawa wani ƙauyen Arsal da ke ƙasar Lebanon, inda suka hallaka wasu jami'an tsaro tare kuma da yin garkuwa da wasu daga cikinsu. 'Yan tawayen sun ce a shirye suke, su yi musayar jami'an tsaron da suka kama da 'yan uwan nasu da gwamnatin Lebanon ke tsare da su.

Jami'an tsaron Lebanon ɗin sun tabbatar da wannan labarin har ma suka ce 'yan tawayen na Siriya sun kame ofishin 'yan sanda. To sai dai sojin ƙasar sun ce ba za su zuba idanu suna kallon 'yan tawayen na Siriya na yin wannan aika-aika ba.

Mawallafi : Ahmed Salisu
Edita : Abdourahamane Hassane