1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

'Yan tawayen Mali sun kafa sabon kawance

May 3, 2024

Manyan kungiyoyin 'yan tawaye da ke da'awar ballewar yankin Azawad da ke arewacin Mali sun sanar da kafa wani sabon kawance tare da bayyana wani mutum a matsayin jagora.

https://p.dw.com/p/4fSQi
'Yan tawayen Mali sun kafa sabon kawance
'Yan tawayen Mali sun kafa sabon kawanceHoto: Souleymane Ag Anara/AFP

A wata sanarwar  da 'yan tawayen Abzinawan da suka fice daga yarjejeniyar birnin Aligiers suka fitar da yammacin ranar Alhamis 02.05.2024, sun ce sabon kawancen mai lakabi da 'Cadre stratégique permanent pour la défense du peuple de l'Azawad' wato (CSP-DPA) na karkashin jagorancin Bilal Ag Acherif.

Shi dai Bilal Ag Acherif ya kasance kusa na masu fafutukar darewar Mali gida biyu, kuma a watan Maris din da ya gabata gwamnatin mulkin sojin kasar ta kakaba masa takunkumi.

Karin bayani: Mali ta soke yarjejeniya da 'yan tawayen Abzinawa

Wannan dai na zuwa ne watanni kadan bayan da sojojin Mali suka fatattaki 'yan tawayen Abzinawan daga yankunan da suke da iko da su a arewacin kasar a yayin wani gagarumin farmaki da suka kai tare da kame birnin Kidal da ya share shekaru a hannun kungiyoyi masu da'awar neman 'yancin cin gishi kan yankin.