1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Kwango: M23 ta kwace birnin Goma

January 27, 2025

Majiyoyin tsaro masu kusanci da MDD sun ce 'yan tawayen M23 wanda sojojin Ruwanda kusan 4,000 ke dafa wa sun kutsa cikin birnin Goma da ke gabashin Kwango

https://p.dw.com/p/4pfLn
DR Kongo | M23 Rebellen
Hoto: Arlette Bashizi/REUTERS

Birnin Goma birnin mafi girma a gabashin Kwango ya wayi safiyar wannan Litinin cikin hannun 'yan tawayen M23 da sojojin Ruwanda bayan shafe dogon lokaci ana bata kashi cikin yayani na zazzafar takaddamar diflomasiyya.

Wasu majiyoyin tsaro masu kusanci da Majalisar Dinkin Duniya sun bayyana cewa 'yan tawayen M23 wanda sojojin Ruwanda kusan 4,000 ke dafawa sun kutsa cikin birnin da yammacin jiya Lahadi inda aka yi ta jin karar mayan makamai tare da tsayar da al'amura cik.

Karin bayani: Jamhuriyar Demokuradiyyar Kwango za ta yi sulhu da Ruwanda

Wannan yanayi da aka shiga ya sa shugaban kasar Kenya William Ruto kiran taron gaggawa na musamman na kungiyar kasashen gabashin Afirka a sa'o'i 48 masu zuwa tare da gayyatar shugabannin Kwango da Ruwanda wato Felix Tschisekedi da takwaransa Paul Kagame.

Karin bayani: MDD ta bukaci Rwanda ta janye dakarunta a Kwango

Dama dai a maraicen jiya Lahadi bayan wani taro, kwamitin sulhu na MDD ya yi Allah wadai da take-taken Ruwanda na keta haddin kasa mai cikakken 'yanci tare da bukatarta da ta gaggauta janye dakarunta daga gabashin Jamhuriyar Kwango.