1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan tawaye sun kai harin rokoki a yankin Kordofan ta Kudu

October 8, 2012

Aƙalla mutum ɗaya ya mutu sannan uku sun samu raunuka a harin da 'yan tawaye suka kai a jihar Kordofan ta Kudu mai arzikin man fetir dake kusa da iyakar Sudan ta Kudu.

https://p.dw.com/p/16MLM
Hoto: Reuters

An yi harbe harbe tare da amfani da rokoki a birnin Kadugli hedlwatar jihar Kordofan ta kudu kusa da kan iyaka da Sudan ta kudu. Fiye da shekara guda kenan sojojin Sudan suke fafata wa da 'yan tawaye a jihar mai arzikin man fetir, amma faɗan bai taɓa kai birnin Kadugli. Wani jami'in asusun UNICEF mai ofishi a birnin ya ce an kwashe misalin mintoci 30 ana ɓarin wuta da hantsin wannan Litinin. Ɗaya daga cikin rokokin ya faɗi a harabar asusun na UNICEF sai dai bai fashe ba, amma mace ɗaya ta samu rauni sakamakon fashewar wani makami mai linzami a wajen harabar. Aƙalla mutum ɗaya ya mutu sannan uku sun samu raunuka a harin da 'yan tawaye suka kai a jihar ta Kordofan ta Kudu. 'Yan tawaye dake faɗa a Kordofan ta Kudu sun zama abin damuwa tsakanin Sudan ad Sudan ta Kudu tun bayan rabuwar su a cikin watan Yulin bara, ƙarƙashin wata yarjejeniyar zaman lafiya ta 2005 wadda ta kawo ƙarshen yaƙin basasan shekaru gommai.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe