1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan ta'adda sun kai harin bam a Somaliya

May 8, 2017

Kunigyar Al Shabaab ta kaddamar da hari a fadar gwamnatin kasar Somaliya inda aka samu salwantar rayuka da ma jikkatar wasu mutane da yammacin ranar Litinin.

https://p.dw.com/p/2cdG8
Somalia Autobombe-Überfall in Mogadishu
Hoto: picture-alliance/dpa/S. Y. Warsame

Rahotanni na cewa akalla mutane shida ne suka muta yayin da wasu goma kuma suka ji jiki a wani harin bam da aka kai a Mogadishu babban birnin kasar.

Rundunar jami'an 'yan sandan kasar ta ce harin ya faru ne lokacin da wata mota dauke da nakiyoyi ta tarwatse a wani wajen da ke kusa da ofishin hukumar shige da ficen kasar. Tuni kuwa kungiyar Al Shabaab ta dauki alhakin harin na ranar Litinin, kungiya ta tarzomar cikin gida mai alaka da Al Qaeda.

Mayakan na Al Shabaab dai sun yi kaurin suna da kaddamar da munanan hare-hare a birnin na Mogadishu da ma ratsin wasu garuruwa na kasar.