1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan Sudan na ci gaba da bore a Khartum

Abdoulaye Mamane Amadou MAB
October 27, 2022

Jami'an tsaron Sudan sun yi amfani da hayaki mai sa kwalla wajen tarwatsa masu boren rajin girka dimukuradiyya da suka fito zanga-zanga a ranar Alhamis.

https://p.dw.com/p/4ImCV
Proteste im Sudan
Hoto: Marwan Ali/AP/dpa/picture alliance

Masu aiko da rahotanni sun ce an ga hayakin gurneti ya turnike arewacin babban birnin kasar Khartum a yayin da dubban masu boren suka kafa shingaye, a hankorinsu na neman ko ana ha maza ha mata a dawo da mulkin farar hula a kasar.

Tun bayan da Janar Abdel Fattah al-Burhane ya karbe mulki da tsinin bindiga daga wata gwamnatin farar hula, zanga-zangar adawa da salon mulkinsa ta karade wannan kasa, tare da zama silar mutuwar mutane da dama. Ko a unguwar al-Deim kadai da ke kudancin birnin Khartum da masu boren suka yi tattaki a wannan rana, an kashe akalla masu zanga-zanga 119 a cikin tsukin shekara guda.