1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan Saudi na son a shirya da Isra'ila - Pompeo

Ahmed Salisu
February 28, 2021

Tsohon sakataren harkokin wajen Amirka Mike Pompeo ya ce 'yan Saudiyya da dama na son ganin an kawar da tsamin dangantakar da ke akwai tsakanin kasar da Isra'ila.

https://p.dw.com/p/3q2I9
USA Außenminister Pompeo Kubapolitik
Hoto: Saul Loeb/REUTERS

Pompeo ya yi wadannan kalaman ne gabannin wani taro da aka shirya don yaki da kin jinin Yahudawa wanda a lokacin ne zai karbi wata lambar girma irinta ta farko da taron zai bayar a gobe Litinin idan Allah ya kaimu.

Baya kuma ga wasu 'yan Saudiyya da ya ce suna a daidaita da Isra'ilan, tsohon sakataren na harkokin wajen Amirkan ya ce wasu kasashe da dama ma na son daidata tsakaninsu da ita din sai dai bai bayyana sunayen kasashen ba.

Ya zuwa yanzu dai mahukuntan Saudiyya ba su mayar da martani kan wadannan kalamai na Pompeo ba.