1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan sandan Turkiyya sun damke wani dan IS

Kamaluddeen SaniNovember 12, 2015

Jami'an 'yan sandan kasar Turkiyya sun sami nasarar cafke Bafaranshe Mehdibend Sa'id a ranar larabar a garin Izmir bayan da ya yi dashen gashi domin badda kama.

https://p.dw.com/p/1H4K9
Türkei stellt Medienkonzern unter staatliche Aufsicht - Proteste
Hoto: picture-alliance/AP Photo

Majiyar 'yan sandan ta bayyana cewar mutum mai suna Mehdibend Sa'id, an sanya masa idanu bayan ya shiga cikin kasar Syriya a inda yake yunkurin gudanar da ayyukan ta'addanci a kasar Turkiya. An dai dmnkesh ine a wani gari mai suna Izmir bayan da jami'an leken asirin yankin suka sanar da jami'an tsaro.

Jami'an tsaron Turkiyya na daukar matakan kakkabe wadanda suke da alaka da kungiyar 'yan jihadi tun lokacin da aka hallaka mutane da dama a wani harin kunar bakin wake da aka kai a tsakiyar birnin Ankara na Turkiya da mayakan Is suka kai.