1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan sandan Nijar sun sauya salon fadakarwa

Salissou Boukari MAB
January 25, 2022

Wani salon fadakarwa da 'yan sandan Nijar suka dauka na yin hannunka mai sanda kafin daukar matakin doka ya soma sanya farin ciki da gamsuwa a zukatan matasan da iyayen yara saboda yana samar da kyakkyawar fahimta .

https://p.dw.com/p/463UZ
DW Still | Polizistin in Nigeria | Hassane Haousseize Zouera
Kwamishiyar 'yan sanda Hassane Zouera na taka wara wajen yaki da shaye-shayeHoto: DW

Wannan mataki da hukumar 'yan sanda mai kula da kariyar mata da yara kanana ta dauka na fadakar da matasa, mataki ne na gyara kayanka wanda ba zai zama sauke mu raba ba, domin kuwa iyaye da sauran al'umma ne ya kamata su yi wannan aiki.

Jama'a na kallon wannan mataki da kwamishiniyar 'yan sanda Zouera Hassane da ma'aikatarta ta dauka a matsayin sabon salo, inda suke cewa mai zai hana kowane bangare ya dauki wannan tsari a matsayin abun da ya kamata a bai wa karfi domin kusanto jami'an tsaro da al'umma.  Sidi Mohamed, mamba a majalisar matasa ta kasar Nijar ya ce idan al'umma ta hafimta karuwar kowa ne.

Niger Protest gegen Ergebnis der Präsidentschaftswahl
Matasan NIjar sun saba shiga zanga-zangar siyasa ko ta dalibai

Masana zamantakewar al'umma na ganin cewa baya ga wannan batu mai mahimmanci na fadakarwa da ilimantarwa, hukunci ma batu ne da ya kamata a duba shi da idanun basira. Mai shigar da kara na gwamnati mai shari'a Chaibou Moussa ya ce idan ana hukunta wani yayin da wani kuma na yawonsa duk da cewa laifi guda suka aikata, hakan na sanya wasu masu aikata laifin na kangarewa.

Sai dai babban mai shigar da kara na gwamnati ya ce babu gudu babu ja baya wajen hukunta matasa da ke daukan motoci suna wasanni a cikin gari da su, wanda wani lokaci suke kashe mutane ko jikkatawa shi, lamarin da mai shari'a Chaibou Moussa ya ce babu wani sassauci ga masu wannan gangancin.