1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan sanda sun bankado barazanar hari a Jamus

October 9, 2023

Rufe filin jirgin sama na Hamburg ya faru ne bayan samun wani sakon Email da ke barazanar kai wa jirgin hari, jirgin ya taso ne daga birnin Tehran na kasar Iran zuwa birnin Hamburg.

https://p.dw.com/p/4XJW1
Motocin 'yan sanda a filin sauka da tashin jiragen sama na Hamburg
Motocin 'yan sanda a filin sauka da tashin jiragen sama na HamburgHoto: Jonas Walzberg/dpa/picture alliance

Hada-hada ta koma daidai a filin jirgin saman birnin Hamburg da ke arewacin kasar Jamus, bayan tsaikon da aka samu na tsawon sa'o'i kalilan a ranar Litinin kan barazanar tsaro. Wannan ya biyo bayan samun wani sakon Email da ke nuna yuwuwar kai hari a cikin wani jirgin sama da ya taso daga birnin Tehran na kasar Iran zuwa Hamburg.

Jami'an 'yan sanda sun tabbatar da ganin sakon da aka aiko, inda suka killace fasinjojin jirgin su 198 da ma'aikatansa 16 tare da gudanar da bincike a kansu da kuma kayayyakinsu baki-daya bayan da jirgin ya sauka.

Ko da yake babu wani cikakken bayani da suka fitar a kan al'amarin, sai dai an dai dakatar da sufurin jirage a filin baki-daya domin gudanar da binciken kafin daga bisani a koma hada-hada kamar yadda aka saba.