1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan sandan kasar Jamus sun cafke Djaber Albakr a Leipzig

Salissou Boukari
October 10, 2016

Da sanyin safiyar wannan Litinin din 'yan sandan na Jamus suka sanar da cafke Djaber Albakr dan kasar siriyan nan, da ake zargi da shirin kai hari bayan da aka samu tarin abubuwa masu fashewa a gidansa.

https://p.dw.com/p/2R3zY
Deutschland Gesuchter Islamist in Leipzig festgenommen
Hoto: picture-alliance/dpa/J. Woitas

'Yan sandan kasar Jamus sun yi nasarar cafke Djaber Albakr da ke zaman dan gudun hijira daga kasar Siriya, wanda kuma suke nema ruwa a jallo tun bisa zarginsa na yunkurin kai wani harin ta'addanci a kasar ta Jamus. Rundunar 'yan sandan ta sanar a shafinta na Twitter inda ta ce: "Ta ji dadi gaya bisa samun nasarar cafke Albakr, aikin na tsahon kwanaki biyu akwai wahala lalle, amma kuma tana mai farincikin sanar da cewa ta yi nasarar kame wanda ake zargin a birnin Leipzig." 'Yan sandan na Jamus dai sun tsunduma neman Djaber Albakr dan kasar ta Siriya mai shekaru 22 a duniya ne, bayan da aka samu tarin wasu ababe masu fashewa a gidansa da ke birnin Chemnitz.