'Yan Mozambik na guduwa zuwa kasar Malawi
January 3, 2025Tun kafin majalisar kundin tsarin mulkin Mozambik ta tabbatar da nasarar dan takarar jam'iyar da ke rike da madafun iko na tsawon shekaru wato Frelimo, mutane suka fara tururwa zuwa kasashe makwabta domin gudun abinda ka iya faruwa na rikicin bayan zabe.
Jam'iyyar adawar dai ta yi watsi da sakamakon zaben inda ta kira shi kagagge mai cike da zamba tare da nuna 'yar yatsa ga kotun kolin kasar a irin shari'u da ta ke gudanarwa musamman na siyasa.
Ellen Kaosa na daya daga cikin 'yan gudun hijira 13,000 'yan Mozambik da suka samu mafaka a garin Nsanje da ke iyaka da Malawi ta kudancin kasar. Kaosa da kuma sauran iyalinta sun rugo nan ne tun a ranar da kotun koli ta tabbatar da nasarar jam'iyya mai mulki a zaben da ya gabata mai cike da rudani.
Ta fada wa DW cewa da ita da 'yan uwanta sun ratsa ta cikin hanyoyi masu hadarin gaske ciki har da kogin Zambezi a cikin kwale-kwale kafin isowa Malawi.
"Ta ce na iso nan ne tun a ranar Litinin 23 ga watan Disamba, kuma kamar sauran wadanda suka guje wa rikicin siyasa ni ma na fuskanci matsaloli a wannan sansanin. Ban ci abinci ba, ina da yara sannan wasu matan suna da juna biyu, wasu sofaffi ne, wasu kuma masu bukata ta musamman. Bamu da bandakuna, ruwa da kuma gidajen sauro. Wasu masu kirki sun bamu kofi daidaya na kunu a ranar da muka iso, ba abu ne da zai isa ba. cututtuka irin su zazzabin cizon sauro da wadanda ake sha a ruwa za su iya kama mu ganin yadda ake ta ruwan sama. Babban dalilin da ya sa muka tsere zuwa Malawi shi ne mu ceci rayukanmu, sai dai muna neman taimako a bangarorin abinci da wurin kwana saboda kwana cikin tantuna akwai matukar zafi."
Wasu daga cikin matan sun ce basu ma san inda mazajensu suke ba wata kila sun kama wata hanyar ta daban ko kuma rikici ya rutsa da su.
Kwamishinan yankin Nsanje Dominic Mwandira ya ce lamarin da 'yan gudun hijirar ke ciki babu dadi kuma ya rubuta wa babban ministan da ke kula da 'yan gudun hijira na kasar don sanar da shi halin da ake ciki.
Masu fafutukar kare hakkin bil Adama dai sun bukaci Malawi da kuma kasashen duniya su mayar da hankali kan walwalar mata da tsofaffi da masu bukata ta musamman da kuma yara kanana.
Moses Mkandawire shi ne daraktan cibiyar Nyika da ke bibiyar halin da 'yan gudun hijira ke ciki a kasar, ya ce akwai bukatar aiki tare domin samar da zaman lafiya mai dorewa.
"Abinda nake nema shi ne kasashen duniya da shugabannin kungiyar kasashen yankinmu na SADC su yi aiki tare su fada wa hukumomin Mozambik da kuma shugabannin adawa cewa zaman lafiya ya fi zama dan sarki, Yanzu abin da za mu iya yi a matsayinmu na kasa shi ne mu samar musu da abinci da barguna da sauran kayan agaji shi ne mafi muhimmanci abu na karshe shin ne Malawi ta kasance cikin kwamitin kasashen SADC da za su yi wa abokanmu na Mozambik magana saboda wadannan 'yan uwan namu su koma yankunansu domin sake fara rayuwarsu a can".
Hukumomin Malawi dai sun tabbatar cewa suna aiki tare da hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya UNHCR domin duba abin da 'yan gudun hijirar na Mozambik suke bukata.
Mai magana da yawun gundumar Nsanje Robert Naija, ya shaida wa DW cewa Malawi ta samar da daruruwan buhuhunan masara da fulawa da wake ga 'yan gudun hijirar.
"Ya zuwa yanzu mun samar wa 'yan gudun hijirar mafaka, wasu na nan a wuraren da muka tanadar wasu kuma na makarantun firamare, kuma muna shirye-shiryen sauya wa wadanda ke makarantun matsuguni zuwa wasu wurare a yayin da muke aiki da ma'aikatar kula da aukuwar bala'o'i bayan ta samar da buhuhunan masara da na fulawa masu nauyin kilogiram 25 har guda 350. Ga wake ma an kawo musu sannan mun sanar wa ma'aikatar tsaron cikin gida, wannan shi ne hali da ake ciki yanzu haka".
A yanzu dai ana sa ran rantsar da dan takarar jam'iyya mai mulki Frelimo Daniel Chapo a matsayin shugaban kasar Mozambik a ranar 15 ga watan Janairu. Majalisar Kundin tsarin mulkin kasar ta ce Chapo ya lashe zaben shugaban kasar na 9 ga Oktoban 2024 da kusan kashi 65% cikin dari na kuri'un da aka kada.
A yayin da ta ce shi kuma dan takarar adawa Venancio Mondlane ya samu kaso 24% cikin dari na kuri'un da masu zabe suka kada a zaben na Mozambik.