Rasha: Bukatar ladabtar da wasu jami'an soji
January 3, 2023Al'ummar Rasha da ma wasu 'yan majalisar kasar sun bukaci a dauki matakin ladabtarwa kan wasu dakuru da suka zarga da yin watsi da hadarin da ya tunkaro su yayin da ake ci gaba da tada jijiyoyin wuya kan harin da Ukraine ta kai wanda ya yi sanadiyar mutuwar gomman sojojin Rasha. 'Yan majalisar dokokin sun ce ya kamata a daura alhakin mutuwar dakarun kan kwamandojin kasar.
A cikin sanarwar da Rasha ta fitar, ta ce an kashe dakarunta 63 a daren sabuwar shekara a harin da aka kai wani ginin da ke dauke da sojojinta a yankin Donestsk da ke gabashin Ukraine da Rashar ta mamaye. Harin na jajajibarin sabuwar shekara ya zo ne a yayin da Rasha ke cigaba da kai hare-haren jirage marasa matuka kan manyan biranen Ukraine.
Sai dai a share guda, shugaba Volodmyr Zelensky ya ce akwai fargabar Rasha na shirya kara kai wasu hare-hare na jirage marasa matuka da nufin rusa Ukraine. Shugaba Zelensky ya ce sun sami bayanan da ke nuna cewa Moscow na nufin kara tsawaita hare-harenta da jiragen kirar Iran. Shugaban ya kara da cewa za su dauki dukkan matakan da suka dace wajen ganin sun kawo karshen abun ya ayyana a matsayin ayyukan ta'addanci.
Ukraine ta ce a wannan sabuwar shekarar ta kakkabo kimanin jiragen sama marasa matuka 80.