1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kada kuri'ar zaben sabon shugaban kasar Kenya

August 9, 2022

Miliyoyim 'yan kasar Kenya sun yi zaben shugaban kasa da na 'yan majalisa a fafatawa da ba kasafai ake gani ba, inda shugaban kasa mai barin gado ke marawa dan adawa mafi dadewa a kasar baya a maimakon mataimakinsa.

https://p.dw.com/p/4FKdO
Kenia Wahlen Raila Odinga William Ruto
Hoto: AFP

Masu kada kuri'a sun yi jerin gwano bisa tsari tun wayewar gari zuwa yammacin Litinin, domin kada kuri'unsu a zaben da ke zama zakaran gwajin dafi, na tabbatar da dimokuradiyya a kasar, inda talakawa ke kara nuna rashin gamsuwa da kamun ludayin shugabannin siyasa. An dai samu jinkirin bude rumfunan zabe a wasu mazabu saboda tangardar na'urar zabe,amma Shugaban kasar Uhuru Kenyatta mai barin gado bayan wa'adin shugabanci biyu, ya bayyana gamsuwar sa kan yadda zaben ya gudana.

Daya daga cikin abin da ke dauki hankali a zaben na bana a Kenya, shi ne fafatawa tsakanin mataimakin shugaban kasa wanda ya tsaya takara William Ruto, mai shekaru 55, da Raila Odinga, tsohon madugun 'yan adawa mai shekaru 77 da haihuwa wanda kuma ke samun goyon bayan Shugaba Uhuru Kenyatta. Ana dai fargabar rashin amincewa da sakamako daga wani bangare, lamarin da ka iya haifar da rikicin bayan zabe. Masu sa ido na kasa da kasa fiye da 160 ciki har da na tarayyar Afirka sun shaida yadda zaben gama garin ya gudana.

Kenia Kibera Slum Nairobi Wahlen
Hoto: Monicah Mwangi/REUTERS

An dai tsaurara matakan tsaro a fadin Kenya, da jami'ai fiye da 150,000 a wani mataki na kaucewa rikicin zabe da ya faru a 2007 wanda ya yi sanadiyyar rasa rayuka sama da 1,000. Mutane miliyan 22 da suka yi rejistar zaben na bana, na fatan zaben zai kawo sauyin tsaro da ma inganta rayuwar 'yan kasar kusan miliyan 50.

Yanzu haka dai hukumar zaben kasar Kenya IEBC, na shan matsin lamba don tabbatar da sahihin zabe a dukkanin zabukan  shugaban kasa da na 'yan majalisar dattawa da gwamnoni da 'yan majalisa da wakilan mata da wasu jami'an kananan hukumomi. Sai dai hukumar, wacce ta kashe kusan dala miliyan 350 a shirya zaben, ta ce na'urorin zaben kusan 200 sun samu matsala, ta kuma dage zabe a yankin wajen mai iyaka da Somaliya saboda harbin bindigogi.

Yayin da za a fara zuba ido kan sakamako a kwanaki masu zuwa, akwai yuwuwar shiga zagaye na biyu na zaben idan ba dan takarar da ya samu fiye kashi 50 cikin 100 na kuri'u. Kuma manyan kalubale da ke jiran sabon shugaba sun hada da magance tsadar rayuwa da rashin aikin matasa da yaki da cin hanci sai tulin bashin da ke kan kasar da kusan dala biliyan 70.