1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan hamayyar Siriya a Jamus

January 5, 2012

'Yan hamayyar Siriya dake balaguron Jamus sun bayyana fatan samun cikakken goyan baya daga gwamnatin ƙasar.

https://p.dw.com/p/13ezh
Demonstrators protest against Syria's President Bashar al-Assad in Idlib January 2, 2012. The banner in the centre reads "The price of freedom very expensive, we ready". Picture taken January 2, 2012. REUTERS/Handout (SYRIA - Tags: POLITICS CIVIL UNREST) THIS IMAGE HAS BEEN SUPPLIED BY A THIRD PARTY. IT IS DISTRIBUTED, EXACTLY AS RECEIVED BY REUTERS, AS A SERVICE TO CLIENTS
Masu zanga-zangar adawa da gwamnatin SiriyaHoto: Reuters

A wani taron da suka gudanar da manema labarai a Berlin, a ziyarar da suke yi ga Jamus, 'yan hamayyar ƙasar Siriya sun bayyana fatan samun goyan baya daga ƙetare domin dakatar da tsauraran matakan da jami'an tsaron Siriyar ke ɗauka, wanda kawo yanzu yayi sanadiyyar rayukan mutane sama da dubu shida a ƙasar.

A fafutukarsu ta neman ganin bayan mulkin shugaba Bashar al-Assad a sar Siriya da kuma maye gurbinsa da wani zaɓaɓɓen shugaba, 'yan hamayyar dake balaguron ƙasashen ƙetare don neman goyan baya, sun saka dogon buri akan Jamus, kamar yadda aka ji daga bakin Hozan Ibrahim mai shekaru 28 da haifuwa da yayi kimanin shekara ɗaya a gidan kaso yake kuma ɗaya daga cikin gaggan shuagabannin majalisar ƙasa da 'yan hamayyar suka kafa:

Hozan Ibrahim, Mitglied im Generalsekretariat des Syrian National Councils, spricht am Mittwoch (04.01.2012) auf der Bundespressekonferenz in Berlin. Thema war der Aufstand in Syrien und die Unterstützung des friedlichen Aufstands durch die deutsche Zivilgesellschaft. Foto: Sebastian Kahnert dpa/lbn
Hozan Ibrahim, wakili a majalisar ƙasa ta 'yan adawar siriyaHoto: picture-alliance/dpa

"Abin da muke buƙata daga gwamnatin Jamus shi ne tayi amanna da majalisarn ƙasar Siriya ta 'yan hamayya a matsayin mai magana da yawun talakawan Siriya ta kuma janye jakadanta daga Damascus."

Ita dai majalisar ta Siriya, wadda aka kafa ta a watan agustan da ya wuce, ta ƙunshi ƙungiyoyi ne na 'yan hamayya daban-daban a cikin gida da wajen Siriyar. Farfesa Burhan Ghalioun, maim koyarwa a jami'ar Sorbon ta Faransa, shi ne shugaban majalisar. A saboda manufofi na tsaro ba a bayyana sunayen wakilan majalisar da har yanzu suke can Siriya ba. A watan desamban da ya wuce ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle ya gana da uku daga cikin wakilanta, abin da ya haɗa har da Hozan Ibrahim. Sai dai kuma duk da haka gwamnatin Jamus na ɗariɗari da buƙatar da 'yan hamayyar suka gabatar. Bisa ga ra'ayin gwamnatin matakai na takunkumi sune mafi a'ala a wannan halin da muke ciki yanzun. Amma jami'in siyasar the Greens kuma wakili a majalisar ƙasa ta Siriyar, Fehrad Ahma na ganin hakan ba zata wadatar ba. Ya bukaci da a shata wani yanki na tsaro a dab da iyakar Turkiyya, inda mutane zasu samu kafar neman mafaka.

Ferhad Ahma, member of the Syrian National Council speaks during a news conference at the Federal Press Conference in Berlin January 4, 2012. REUTERS/Thomas Peter (GERMANY - Tags: POLITICS HEADSHOT)
Ferhad Ahma, wakilin majalisar ƙasa ta Siriya kuma jami'in jam'iyyar the GreensHoto: Reuters

"A halin da ake ciki yanzu mai yiwuwa nan gaba dakarun sojan da suka yi wa rundunar sojan Siriya huruji su shiga yaƙin sunƙuru, lamarin da zai ƙara jefa talakawan Siriyar cikin mawuyacin hali na ƙaƙa-nika-yi, muddin kafofi na ƙasa da ƙasa suka ci gaba da yin sako-sako da lamarin kamar yadda muke gani yanzun."

Ita dai gwamnatin Siriya kusan tana da jami'anta na leƙen asiri kusan a dukkan sassa na duniya, waɗanda kuma ba su shayin kai hari kan abokan adawa a ƙetare, kamar yadda shi kansa jami'in jam'iyyar the Greens Fehrad Ahma ya jita a jika. A wajejen ƙarshen watan da ya wuce wasu da ba a san ko su wane ne ba sun kai masa hari suka kuma lallasa shi a gidansa. Mahukunta dai na ci gaba da bin bahasin wannan ta'adi. A can Siriyar ma dai danginsa sun sha fama da barazana a shekarun baya-bayan nan an kuma labarta musu cewar ana bin diddigin kai da komonsa a nan Jamus. Ba shakka gwamnatin Siriya zata ƙara tsaurara irin waɗannan matakai, musamman dangane da barazanar da take fuskanta game da makomarta a halin yanzu.

Mawallafi: Nina Werkhäuser/Ahmad Tijani Lawal

Edita: Muhammed Nasiru Awal

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani