1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan gudun hijirar Ukraine sun kai miliyan daya

March 3, 2022

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce yawan mutanen da suka yi kaura daga Ukraine tun bayan da Rasha ta kaddamar da mamayar kasar sun kai miliyan daya.

https://p.dw.com/p/47vsA
Tausende Menschen warten am Übergang von Uschhorod in der Slowakei
Hoto: Luboš Palata/DW

Adadin a cewar hukumar kula da 'yan gudun hijirar ta Majalisar Dinkin Duniya ya kai kashi biyu cikin dari na al'ummar Ukraine wanda Bankin duniya ya ce sun kai mutum miliyan 44

Shugaban hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya Flippo Grandi ya ce mutane na ta kwarara zuwa kasashe makwabta.

Rasha ta cigaba da luguden wuta a biranen Ukraine da suka hada da Kharkiv da Mariupol yayin da ta kama birnin Kherson a ranar Laraba ta na kuma cigaba da kokarin dannawa zuwa birnin Kiev.

A safiyar wannan Alhamis an bukaci mazauna birnin na Kieve su je wuraren buya mafi kusa da su. Wasu hotunan bidiyo da aka yada a shafukan sada zumunta sun nuna yadda mayan abubuwan fashewa ke fadawa a birnin. 

A waje guda kuma babban mai gabatar da kara na kotun duniya ta ICC Karim AA Khan ya ce zai kaddamar da binciken tafka laifukan yaki da aka aikata akan jama'a fararen hula a Ukraine.