'Yan gudun hijirar Siriya sun shiga halin ni 'ya su a Masar
November 14, 2012Kwararrun sun bayyanar da cewa yawansu zai karu zuwa dubu 700 kafin karshen shekarar 2012. A dai halin yanzu 'yan gudun hijrar Siriya kimanin dubu 300 ke zaune a kasashen Turkiya da Jordan da Libanon da kuma Iraki. Kuma ko da yake shugaba Mohammed Mursi ya yi alkawarin ba da taimako ga 'yan gudun hijirar Siriya da ke zaune a kasarsa, to amma 'yan gudun hijrar sun ce sun gaji da gafara sa ba su ga kaho ba.
Matsalar rashin kudin jiyya
Fatima wata 'yar gudun hijira ce daga Siriya da ke kwance kan gadon jiyya inda take shakar iskar Oxygen cikin kowane dakiku shida saboda cewa ita kanta ba ta iya numfashi. Ita dai wannan mata da taimakon mijinta ne ta dan daga rigarta domin gwada wani babban tabo da ke bayanta.Ta ce:
" Wannan tabo na same shi daga wani albarushi da ya taba ni har sai da ya kai ga hantata. Sai da aka rede rabin hantata ta dama kuma ita ta hagun bata aiki sosai sai da naurar shakar Oxygen. Ina fatan samun sauki saboda cewa 'ya'yana ba su girma ba."
Ita dai wannan mata mai 'ya'ya biyu ta ci karo da harbin bindiga a cikin wata musayar wuta da aka yi tsakanin dakarun gwamnati da 'yan tawaye a birnin Homs. Jim kadan bayan hakan ne kuma aka yi luguden wuta a unguwar da take- dalilin da ya sa ta arce zuwa birnin Alkahiran Masar tare da iyalinta. Fatima ta ce:
" Mun gudu ne ba tare mun dauki wani abu ba. Ba mu da tufafen da za su ba kariya daga sanyin hunturu. Ba mu da komai."
Shi kuma mijinta cewa yake: "Na zo da kudin da na ajiye amma na kashe su wajen biyan kudin asibiti da sayen magunguna. Wannan maganin na saye shi kan Fan 700 na Masar kwatankwancin Euro 100. Matata na bukatar sabbin kaya.To amma muna rashin kudi. Ko da yake an yi mana karo-karo a masallaci, to amma har yanzu babu wani taimako da muka samu a nan Masar."
Mursi ya saba alkawari
Shi dai shugaban Masar Mohammed Mursi a cikin jawabansa na gidan telebijan ya sha shan alwashin ba da taimakon gaggawa ga 'yan siriya da ya ce suna zaman tamkar 'yanuwa a gareshi.
"Kullum zancen kenan.To amma wa ya taimka wa 'yan uwa daga Siriya? Babu wani taimako da muka samu ya zuwa yanzu."
Mohammed ya na bayyana fushinsa game da rashin cika wannan alkawari. Wannan mutun haifaffen kasar Siriya tun shekaru 15 da suka gabata ne yake zaune a Jamus. To amma ya je birnin Alkahira ne domin ya taimaka wa danginsa da suka baro birnin Homs. Kimanin 'yan gudun hijrar Siriya guda 250 ne dai yake bai wa taimako a jefe-jefe ta shirya musu wajen barci da abinci da kuma tufafi daga kudin tallafi da yake samu daga cocin Katolila ta Laurentius da ke birnin Berlin. Kuma babu wani abu da gwamnatin Masar da hukumar kula da 'yan gudun hijra ta Majalisar Dinkin Duniya(UNHCR) da ya tuntuba suka yi domin ba 'yan gudun hijrar takardun izinin zama.
Mohammed ya kara da cewa: Ana magana ne game da 'yan kasar Siriya da ke Libanon daTurkiya da Jordan. To amma ba wanda ke ba da kulawa ga 'yan kasar Siriya masu yawan kimanin dubu 150 dake zaune a Masar."
Za a iya sauraron sautin wannan rahoto daga kasa.
Mawallafiya: Cornelia Wegerhoff/ Halima Balaraba Abbas
Edita: MohammadNasiru Awal