1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yuganda ta karbi 'yan gudun hijirar Afghanistan

Ramatu Garba Baba
August 25, 2021

'Yan gudun hijirar kasar Afghanistan kimanin 51 aka sauke a wannan Laraba a kasar Yuganda. Suna daga cikin rukunin farko da kasar ta amince ta bai wa mafaka.

https://p.dw.com/p/3zU1o
Iran | Coronavirus | Eid al-Fitr
Hoto: Morteza Nikoubazl/NurPhoto/picture alliance

Sabanin fargaba da jama'a suka nuna a game da shigo musu da masu tsatsaurar ra'ayin addini, gwamnatin Yugandan ta ce, an tantance su kuma za a tsugunar da 'yan gudun hijirar ne na wani dan lokaci, kafin a tanadar musu wurin zama na dindindin a Amirka dama sauran kasashen Turai.

Tun bayan da Taliban ta kwace iko a Afghanistan, kasar ta fada cikin rudani, da dama na tserewa saboda fargabar yadda rayuwa za ta kasance musu a karkashin mulkin Taliban da a baya can ta gasa wa 'yan kasa aya a hannu da sunan mulki da shari'ar musulunci, lamarin da ya sha suka saboda zargin da aka yi na cewa, mulkin na Taliban yayi hannun riga da koyarwar addinin Islama.

 Yuganda da ke gabashin Afrika, ta shahara a bayar da mafaka ga 'yan gudun hijira da ke tsere wa rikici, yanzu haka tana tsugune da 'yan gudun hijira sama da miliyan daya sai dai akasarinsu sun fito ne daga kasar Sudan ta Kudu da rikicin yaki ya daidaita.