1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan gudun hijira na yunkurin kashe kai

Ramatu Garba Baba
May 21, 2019

Wasu 'yan gudun hijira masu neman mafaka a Australiya akalla 10 ne suka yi yunkurin kashe kansu bayan nasarar da jam'iyyar Conservative ta masu ra'ayin rikau mai kin jinin baki ta samu a zaben kasar na makon jiya.

https://p.dw.com/p/3IpyQ
Proteste in australischen Flüchtlingslager 2002
Hoto: AP

'Yan gudun hijira sun kasance cikin zaman tsanmani inda suka yi fatan jam'iyyar Labor mai sassaucin ra'ayi za ta lashe zaben don biya musu bukatunsu na samun mafaka a kasar ta Australiya, wadanda suka yi wannan yunkurin sun fito ne daga kasashen Sudan da Iraki da kuma Iran. Sun yi yunkurin kashe kansu ta hanyar rataya ko cinna wa kansu wuta bayan da jam'iyyar Labor mai sassaucin ra'ayi ta sha kayi a zaben. 

Australiya na daga cikin kasashen Turai, da ta ce ta daina bai wa 'yan gudun hijira da ke isa kasar ta jirgin ruwa izinin zama, ta nemi mayar da su kasashensu na asali ko wasu kasashe da ke da sha'awar karbarsu. Tuni dai kungiyoyin kare hakkin bil adama suka soki wannan lamiri. Yanzu haka 'Yan gudun hijira kusan dari takwas ke jiran tsanmani kafin wannan sakamakon da ya kawo karshen burinsu na rayuwa a Turai.