1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Adadin 'yan gudun hijira na karuwa a Siriya

Abdoulaye Mamane Amadou
December 27, 2019

Fiye da mutane dubu 235 sun kaurace wa gidajensu a kasa ga makonni biyu sakamakon yawaitar ruwan bama-bamai da dakarun Siriya da Rasha ke kaddamarwa.

https://p.dw.com/p/3VOPn
Syrien Idlib | Syrier in Harbanos
Hoto: picture-alliance/AA/M. Said

Wata sanarwar Majalisar Dinkin Duniya ta ce garuruwa da dama sun koma kufai musamman ma a Maaret al-Noomane, inda jama'a suka gudu zuwa garuruwan Ariha da Saraqeb da Idleb domin samun mafaka a sansanonin 'yan gudun hijira wadanda daman suke cike da jama'a, hakan da ma garuruwan da ke kan iyaka da kasar Turkiyya, kana kuma sauran jama'a na garzayawa zuwa wasu yankunan da ke hannun 'yan tawayen na Siriya masu goyon bayan kasar Turkiyya in ji Majalisar Dinkin Duniya.

A shekarar 2011 ne rikicin kasar Siriya ya barke inda kawo yanzu ya halaka fiye da mutane dubu 370. baya ga zama sanadiyar kauracewar wasu miliyoyin jama'a daga gidajensu.