1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutuwar bakln haure a gabar tekun Tunisiya

Abdourahamane Hassane
July 27, 2023

Hukumomi a Tunisiya sun ce bakin haure 800 ne da ke kokarin shiga Turai ba bisa ka'ida ba, suka nutse a gabar tekun kasar a cikin watanni shida na farkon shekara,

https://p.dw.com/p/4UTWn
Migranten wagen trotz Unfällen die Mittelmeerüberfahrt
Hoto: Oliver Weiken/dpa/picture allianc

A cewar wannan majiyar, an gano gawarwakin bakin haure 789 daga cikin tekun, wadanda suka hada da 'yan Tunisiya 102, da wasu 'yan kasashen waje. A watan Yuli da ya gabata Tarayyar Turai da Tunusiya suka amince da wani haɗin gwiwa da nufin hana fataucin mutane da kaura ba bisa ka'ida ba, amma duk da haka ana ci gaba da samun kwararar jama'a.