1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Yan bindiga sun hallaka sojojin Nijar

Ramatu Garba Baba
March 27, 2022

Sojojin Nijar shida wasu 'yan bindiga suka kashe a wani hari da suka kai kan ayarin motocinsu a wani kauye mai suna Kolmane da ke Kudu maso Yammacin kasar Burkina Faso.

https://p.dw.com/p/495lW
Symbolbild | Nigeria | SWAT
Hoto: Imago Images/ZUMA Press/Planetpix/A. F. E. Lii

Ma'aikatar tsaron kasar Burkina Faso ta sanar da mutuwar wasu sojojin Nijar shida, da ake zargin 'yan bindiga ne suka hallaka su a wani harin kwanton bauna da suka kai kan ayarin rundunar sojin a kusa da kauyen Kolmane, akwai kuma mutum guda da harin ya raunata baya ga lalata motoci da maharan suka yi.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, an kaddamar da bincike don gano wadanda keda alhakin kai harin. Kauyen na kusa da kan iyakokin Nijar da Burkina Fason, harin wanda tun ranar Alhamis da ta gabata aka kai shi, ya kasance irinsa na biyu a cikin kwanaki goma. Na makon da ya gabata ma, mutum akalla ashirin ne suka mutu a sakamakon wani hari da ake zargin mayakan jihadi da kai wa kan wata motar safa, lamarin da ke kara baiyana koma bayan da kasashen da ke yankin sahel ke fuskanta na tashe-tashen hankula.