1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan bindiga sun kashe manoma 40 a Borno

Abdul-raheem Hassan MAB
November 28, 2020

Rahotanni daga jihar Borno a yankin Arewa maso gabashin Najeriya na cewa akalla manona 40 sun mutu, a wani harin da ake zargin mayakan Boko Haram da kaiwa.

https://p.dw.com/p/3lxxc
Nigeria | Niedergebrannte Fahrzeuge in Auno
Hoto: Getty Images/AFP/A. Marte

Majiyoyi uku sun tabbatar wa kamfanin dillacin labaran Reuters cewa harin ya faru ne a garin Kwashebe da ke karamar hukumar Jere a jihar Borno yayin da manoman ke girbe amfanin gona da safe.

Yanzu haka dai hukumi sun kaddamar da binciken bin kafa ga maharan, sai dai 'yan sanda da sojoji sun ki cewa komai kan sabon harin. Ana dai danganta tsadar abinci da yawaita kai wa manoma farmaki a gonakinsu a wannan shekara.