1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Ta'addanci

Chadi: 'Yan bindiga sun halaka mutane

Lateefa Mustapha Ja'afar
May 18, 2023

Mutane sama da 10 ne aka tabbatar da cewa sun rasa rayukansu a kudancin Chadi, sakamakon harin 'yan bindiga masu satar shanu.

https://p.dw.com/p/4RXp6
Chadi | Zanga-zanga | N'Djamena
Chadi na zaman guda daga kaksashen Afirka da ke fama da tashe-tashen hankulaHoto: LE VISIONNAIRE/REUTERS

Rundunar sojojin kasar Chadin ce ta tabbatar da hakan, inda ta ce lamarin ya afku ne a daidai lokacin da Chadin ta sanar da cewa za ta hada gwiwa da makwabciyar kasar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya domin magance matsalar masu dauke da makamai. 'Yan binidga masu satar shanun sun farmaki kauyen Mankade da ke gundumar Laramanaye, tare da halaka mutane sama da 10 suka kuma yi awon gaba da shanunsu. Ministan tsaron kasar Daoud Yaya Ibrahim da ya tabbatar da afkuwar lamarin ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa, jami'an tsaro sun bi sawunsu tare da halaka bakwai a cikinsu. Ya kara da cewa sun kuma cafke barayin takwas, tare da kwato shanun da suka sace.