1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan adawar Yuganda sun fita daga kurkuku

June 14, 2021

Kotun soji a birnin Kampala ta bayar da belin magoya bayan jagoran adawar Yuganda Bobi Wine wadanda aka tsare da su tun farkon wannan shekarar, lamarin da 'yan adawa ke ganin cewa an yi ne bisa wata manufa ta siyasa.

https://p.dw.com/p/3uuMt
Uganda Bobi Wine
Hoto: Sumy Sadurni/Getty Images/AFP

Wannan ci-gaban na zuwa ne bayan da aka bayar da belin wasu 17 a watan Mayun da ya gabata, bayan da aka tsare su bisa karya dokar takaita yaduwar annobar corona yayin wani gangami. Kana ake tuhumar wasu da rike makamai duk da cewa dukkansu fararen hula ne.

Tun a shekarar data gabata ne dai jami'an tsaron Yuganda ke tsare da magoya bayan Wine din don yi musu tambayoyi. Sai dai tun wancan lokacin an saki wasu yayin da wasu kuma aka daina jin duriyarsu.

Bobi Wine da ya tsaya takara a babban zaben kasar ya sha kaye ne bayan da sakamakon zabe ya nuna cewa shugaba Museveni ne ya sake lashe kujerar shugabancin kasar.