1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zimbabuwe: Zanga-zangar adawa a Harare

Zainab Mohammed Abubakar
August 16, 2019

'Yan sandan kwantar da tarzoma a Zimbabuwe, sun yi dirar mikiya a kan 'yan adawa da ke zanga-zanga, duk da dokar haramci da gwamnatin shugaba Emmerson Mnangagwa ta gabatar

https://p.dw.com/p/3O2Xy
Simbabwe Harare | Demonstration & Ausschreitungen | Movement for Democratic Change
Hoto: Reuters/P. Bulawayo

Masu gangamin na zargin gwamnatin mai ci da zaluncin da ya shige na hambararriyar gwamnatin Robert Mugabe da ta gabata.

'Yan adawar dai sun yi gangami a dandalin taro da ke birnin Harare, domin kokawa da halin kaka-ni-ka yi da tattalin arzikin kasar ke ciki.

Tun da farko kotun kasar ta haramta gudanar da gangamin, a yayin da aka girke jami'an tsaro a sassa daban daban na babban birnin Zimbabuwe.

Sai dai babbar jam'iyyar adawar kasar ta yi kira ga mayo bayanta dasu kauracewa gangamin, saboda gudun zubar da jini.