1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan adawa sun lashe zaben Istanbul

Ahmed Salisu
June 23, 2019

Jam'iyyar adawa ta CHP ta samu nasara a zaben magajin garin Istanbul inda dan takararta Ekram Imamoglu ya samu nasara kan abokin hamayyarsa na jam'iyyar jam'iyyar AKP Binali Yildrim.

https://p.dw.com/p/3Kxhl
Kommunalwahlen in der Türkei | Ekrem Imamoglu
Hoto: picture-alliance/dpa/AP Photo/L. Pitarakis

A zaben na yau dai Ekram Imamoglu na jam'iyyar adawa ta CHP ya samu kashi 53 cikin 100 na kuri'un da aka kada yayin da tsohon firaministan kasar kana dan takarar jam'iyyar AKP mai mulki Binali Yildrim ya samu kashi 45 cikin 100 na kuri'un.

Tuni da Mr. Yildrim ya amince da shan kaye tare da taya abokin hamayyar tasa murnar lashe zaben, inda ya yi kira gare shi kan  yayi abin da ya dace wajen ciyar da birnin gaba.

Da yake jawabi gaban dubban magoya bayansa, sabon magajin garin ya ce shirye yake ya yi aiki tare da gwamnatin AKP da shugaban kasar Racep Tayyib Erdogan ke jagoranta kana ya jinjinawa al'ummar kasar da ma gwamnati a kokarinsu na kare demokradiyya.

A watan Maris din da ya gabata ne dai aka fara zaben na birnin Istanbul wanda daga bisani jam'iyyar AKP mai mulki ta yi korafin na cewar an tafka kura-kurai, batun da ya sanya hukumar zaben kasar soke shi tare da sanya yau a matsayin rana da za a sake shi.