1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Chadema, ta yi kira ga magoya bayanta da su fito yin bore

Abdoulaye Mamane Amadou MAB
July 31, 2021

Babbar jam'iyyar adawa ta Tanzaniya mai suna Chadema, ta yi kira ga magoya bayanta da su gudanar da zanga -zanga lumana domin yin tir da kama shugabanta da aka yi a Arewa maso yammacin kasar.

https://p.dw.com/p/3yNBA
Tansania Opposition Freeman Mbowe
Freeman Mbowe jagoran 'yan adawa a TanzaniyaHoto: Ericky Boniphace/AFP/Getty Images

Cikin wata sanarwar da ta fitar a wannan Asabar a birnin Dar es Salam , jam'iyyar Chadema ta kara da cewa ta shigar da kara kan "ta'addanci" da ake zargin shugabanta da aikatawa. An dai cafke  Freeman Mbowe da wasu jiga -jigan jam'iyyar Chadema a garin Mwanza tun kwanaki goma da suka gabata a lokacin da suke shirin gudanar da gangami don neman a yi garambawul ga kundin tsarin mulkin Tanzaniya.

Tuni dai wata kotu ta tuhumi  Freeman Mbowe mai shekaru 59 a duniya da zargin hada kai da 'yan ta'adda tare da samar da kudade gudanar da munanan ayyukansu-laifukan da ba sa bayar da damar a yi belinshi.

Wannan kame Mista Mbowe ya tayar da damuwa tsakanin kungiyoyi kare hakkin bil'adama da manyan kasashen yammancin duniya. Amirka ta bukaci shugabar kasar Tanzaniya Samia Suluhu Hassan, wacce ta hau karagar mulki a watan Maris bayan mutuwar John Magufuli, da ta tabbatar da kare 'yancin dukkan 'yan kasa.