1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan adawa a ƙasar Siriya na ƙara matsa ƙaimi

June 3, 2011

Jami'an tsaro sun kashe mutane 34 a garuruwa daban daban inda 'yan adawar suka gudanar da zanga zanga

https://p.dw.com/p/11U3g
Masu zanga zanga a SiriyaHoto: AP/Shaam News Network

Ƙungiyoyin kare hakin bil adama a ƙasar Siriya sun ce kimani mutane guda 34 suka rasa rayukansu yayin da wasu gomai suka jikata a cikin zanga zangar da 'yan adawa na ƙasar suka gudanar. Zanga zangar wacce aka gudanar da ita a cikin garuruwa daban daban da ta tattara mutane kusan dubu ɗari biyu, domin nuna bacin ran su dangane da kisan yara ƙanana da gwamnatin Bashar Alssad take yi,ta kasance mafi samun karɓuwa da aka shirya tun lokacin da aka fara yin yamutsin a tsakiyar watan maris da ya wuce .

To sai dai gidan telbijan na ƙasar ya ce mutane guda ukku ne kwai suka mutu a garin Hama wadanda 'yan sanda suka farma bayan sun kai hari akan wani gini gwamnatin wanda suka cina wa wuta.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Mohammed Nasiru Auwal