1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan adawa 66 sun sake mutuwa a Siriya

January 29, 2012

Siriya ta ƙaddamar da sabbin hare hare akan masu bore da gwamnati

https://p.dw.com/p/13sic
Demonstrators protest against Syria's President Bashar al-Assad in Jerjenaz, near Idlib January 27, 2012. Picture taken January 27, 2012. REUTERS/Handout (SYRIA - Tags: POLITICS CIVIL UNREST) FOR EDITORIAL USE ONLY. NOT FOR SALE FOR MARKETING OR ADVERTISING CAMPAIGNS. THIS IMAGE HAS BEEN SUPPLIED BY A THIRD PARTY. IT IS DISTRIBUTED, EXACTLY AS RECEIVED BY REUTERS, AS A SERVICE TO CLIENTS
Zanga zangar adawa a SiriyaHoto: Reuters

Yini ɗaya kachal bayan da ƙungiyar kasashen Larabawa ta dakatar sanya idon da wata tawagar ta ke yi a ƙasar Siriya, shugaba Bashar al-Assad na ƙasar ya sake ƙaddamar da samamen soji akan 'yan tawayen dake da iko da wasu yankunan dake wajen Damascus babban birnin ƙasar. Ƙungiyoyin kare haƙƙin jama'a sun sanar da cewar an kashe aƙalla mutane 66 a lokacin samamen, ciki kuwa harda fararen hula 26.

A halin da ake ciki kuma, sojojin da suka bijirewa gwamnati sun sake karɓe iko da lardin Homs, mai fama da rigingimu, bayan wani bata kashin da suka yi da dakarun gwamnati a yankin al-Rastan. A wannan asabar ce dai ƙungiyar ƙasashen Larabawar ta dakatar da aikin ayarin ta a ƙasar Siriya saboda tashe tashen hankulan da ke ci gaba da wanzuwa a cikin ƙasar - matakin da kuma hukumomin na Siriya suka bayyana taƙaicin su ga ɗaukar sa, suna masu zargin ƙungiyar da ƙoƙarin yin matsin lamba akan Majalisar Ɗinkin Duniya ta shiga tsakani a rikicin na Siriya.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Abdullahi Tanko Bala