1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yamutsin sojoji a Burkina Faso

April 15, 2011

Mulkin shugaba Blaise Comporé na fuskantar barazana faɗuwa

https://p.dw.com/p/10uEV
Shugaba Burkina Faso Blaise ComporéHoto: picture-alliance/ dpa

Sojoji na gudanar da bore a Ougadougou babban birnin Burkina Faso.Rahotannin sun ce yamutsin wanda dakarun dake tsaron fadar shugaban ƙasar wato Blaise Compaore suke yi , ya bazu zuwa cikin wasu sauran rundunoni sojin guda ukku.Sojojin waɗanda ke ne meman samun biyan buƙatar akan yan kuɗaɗe alahus sun riƙa sintiri akan titi suna yin harbi a sama .

ɗaya daga cikin shaidu wanda bai so bayyana mana sunan sa ba mazaunin birnin Ouagadougou ya bayyanma halin da ake cikin 'Mutane na cikin jin tsoro da fargaba kuma shaguna da kantina sun kasance a rufe'

Tun da farko dai a kwai rahotanin da suka ce shugaban ya fice zuwa ƙauyen su dake da ratan kilomita 30 daga babban birnin ƙasar kafin daga bisanin ya sake dawawo a Ouagadougou

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Usman shehu Usman