1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Aljeriya ta katse hulda diplomasiya da Maroko

Abdourahamane Hassane
August 24, 2021

Aljeriya ta katse hulda diplomasiya da makobciyarta Maroko daidai lokacin da ake ganin kasashen biyu na bukatar juna wajen samun habaka ta tattalin arziki.

https://p.dw.com/p/3zRXZ
Karte Nordafrika Flüchtlinge DE

 

Ministan harkokin waje na Aljeriya ya ce sun katse hulda ne a sakamako kiyyaya da Marokon ke nuna musu. Aljeriyar na zargin moroko da hannu a cikin gobara da aka yi a arewa maso yammacin kasar wacce a ciki mutane 90 suka mutu. Sai dai masu aiko da rahotannin na cewar rikicin bai rasa nasaba da goyon bayan da Maroko ke bai wa 'yan yanki Kabyli na Aljeriya masu neman balewa yayin da Aljeriyar ke ba da goyon baya ga yankin Saraoui na Morokon shi ma mai fafufutkar neman yancin gashin kai.