1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Yamen: Mutane 53 sun kwanta dama

Abdoulaye Mamane Amadou
April 10, 2021

An hallaka mutane 53 a yayin wani batakashi tsakanin 'yan tawayen Hutis da dakarun da ke biyayya ga gawamnati a tsaunukan Kassara da Machjaa mai nisan kilo 120 daga birnin Sanaa.

https://p.dw.com/p/3rotk
Jemen | Huthi Rebellen
Hoto: Getty Images/AFP/G. Noman

Wata majiya ta shedawa kamfanin dillancin labaran AFP da cewar an shafe sa'o'i 24 ana dauki ba dadi a tsaunukan da ke arewacin Mareb, yankin da kuma Allah ya albarkata da dimbin arzikin man fetur, wanda tun a cikin watan Febrairu mayakan Hutis ke neman karbe iko da shi daga hannun sojan gwamnati.

Wannan lamarin na zuwa ne kwanaki bayan bangarori a wannan yanki, na ta linka kira da a tsagaita wutsa tsakanin kawancen sojan da Saudiya ke jagoranta da 'yan tawayen Hutsi masu masun goyon bayan Iran.