1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Yakin Rasha da Ukraine na shafar duniya

Binta Aliyu Zurmi
April 14, 2022

Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira ga kasashen duniya da su yi amfani da matsalar da yakin Rasha da Ukraine ya jefa su wajen karkata ga makamashin da ake sabuntawa.

https://p.dw.com/p/49vIO
Generalsekretär der Vereinten Nationen Antonio Guterres
Hoto: Andrew Kelly/REUTERS

Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya ce yakin da Rasha ke yi da Ukraine na kuntata wa kasashe duniya matalauta ta fannonin rayuwa da dama.

A ganawar da ya yi da manema labaru, Antonio Guterres ya ce kasashen da a baya ke fama da kansu yanzu sun kara shiga cikin hali na matsi, a sabili da hauhawar da farashin kayayyakin masaraufi da ma na makamashi suka yi, wanda a cewar shi ire-iren wadannan kasashen basu murmure daga halin da cutar Covid-19 ta jefa su a baya ba.

Guterres dai na ganin kasashen duniya ya kamata su yi amfani da wannan matsalar wajen maida ta dama ta karkata ga makamashin da ake sabuntawa.