1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Rayuka na salwanta a Zirin Gaza

Abdoulaye Mamane Amadou
October 27, 2023

A daidai lokacin da yakin Hamas da Isra'ila ke kara tsananta Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin yiwuwar kara samun mamata a Gaza saboda rashin shigar da kayan agaji

https://p.dw.com/p/4Y7QD
Hayaki ya turnuke a Zirin Gaza bayan wani luguden wutar da Isra'ila ta yi kan kungiyar Hamas
Hayaki ya turnuke a Zirin Gaza bayan wani luguden wutar da Isra'ila ta yi kan kungiyar HamasHoto: Ali Jadallah/Anadolu/picture alliance

Ma'aikatar lafiyar Falasdinu ta ce ya zuwa yanzu mutane dubu 7.326 ne suka mutu tun bayan kaddamar da farmakin ramuwar gayya da Isra'ila ta yi kan kungiyar Hamas mai iko da Zirin Gaza.

Karin Bayani : Harin bam ya haddasa mace-mace a asibitin Gaza

Rundunar tsaro Isra'ila ta kai wasu jerin hare-hare ta kasa har a kwaryar Zirin Gaza, tare da rakiyar jiragenta na yaki ciki har da marasa matuka, kana rundunar ta ce dakarunta sun yi nasarar komawa gida bayan kutsen ba tare da ko kwarzane ba.

Ita kuwa Amurka na nazari kan yiwuwar kakaba wa Kungiyar Hamas da Iran wasu jerin sabbin takunkumai, wanda ke zaman wani sabon babi na rikicin da ke daukar salo.

Karin Bayani : Zirin Gaza: Goyon baya daga Larabawa

Majalisar Dinkin Duniya dai ta yi gargadin yiwuwar samun karin mamata a Zirin Gaza nan ba da jimawa ba samakaon mamayar da Isra'ila ke yi wa yankin tare da kiran da a gaggauta shigar da kayayakin agaji ga mabukata.