1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yakin EU na safarar bakin haure a teku

Gazali AbdouMay 18, 2015

Kungiyar tarayyar Turai ta EU ta fito da sabon shiri na amfani da na'urorin bincike tare da bincika jiragen ruwa a teku do yaki da safarar mutane zuwa Turai ta teku.

https://p.dw.com/p/1FRdt
EU Mogherini beim EU-Außen- und Verteidigungsministertreffen
Hoto: Reuters/F. Lenoir

Kungiyar Tarayyar Turai ta kaddamar da wani sabon shiri na yaki da masu safarar mutane ta ruwan tekun mediteranean zuwa Turai. Kungiyar ta EU ta kaddamar da wanann shiri a lokacin wani zama da ministocin kula da harkokin kasashen wajen kasashe mambobin kungiyar suka gudanar a yau litanin a birnin Bruxelles.

Shirin wanda kungiyar ta EU ta ce ba a taba yin irinsa ba ya tanadi yin sintiri a saman teku ta hanyar amfani da jiragen yaki da kuma na'urorin bincike. Kazalika shirin na da hurumin tsarewa tare da bincika duk jirgin ruwan da ake zargi da yin safarar bakin haure.

Matakin zai soma aiki gadan- dagan a cikin watan Junin Gobe ko da bai samu lamincewar Majalissar Dinkin Duniya ba. Amma duk wani mataki na yin amfani da karfin soja zai dakaci wani kudiri da ake sa ran Majalissar Dinkin Duniya za ta sanya hannu a kansa a mako mai zuwa.