1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Cece-kuce kan yaki da cin hanci a Jamhuriyar Nijar

Salissou Boukari SB
September 17, 2024

A JAmhuriyar Nijar muhawara ta kaure kan batun yaki da cin hanci da rasha ba sani ba sabo, abin da ake gani ba zai yuwu ba, saboda kusancin wadanda ake zargin da sojojin da suke mulki.

https://p.dw.com/p/4kjMA
Jamhuriyar Nijar | Janar Abdourahamane Tiani shugaban gwamnatin mulkin soja da ya kifar da gwamnatin Mohamed Bazoum
Janar Abdourahamane Tiani shugaban gwamnatin mulkin sojan Jamhuriyar NijarHoto: ORTN/Télé Sahel/AFP/Getty Images

A Jamhuriyar Nijar cece-kuce na masu neman a gurfanar da tsohon shugaban kasa Issoufou Mahamadou da ya mulki kasar tsawon shekaru 10 na dada karuwa, inda wasu ‘yan kasar da dama ke ganin cewa idan har da gaske ne sojojin da suka yi juyin mulki na son tsayar da gaskiya ne da kuma yakar almundahana da dukiyar kasa, sai fa sun nuna ba sani ba sabo, yayin da wasu ke ganin cewa batun kama tsohon shugaban kasar a karkashin doka ba shi da tushe.

Karin Bayani: Nijar: Shekara guda karkashin juyin mulki

Har yanzu za a iya cewa bunnu-bunnu ce wadda taki bunnuwa domin kuwa wannan batu na wasu kungiyoyi da sauran 'yan kasar da ke furta kalaman cewa sai fa an kama tsohon shugaban kasar Issoufou Mahamadou bisa dalillan tafka ta'asa da aka yi a cewar su wadda ta wuce musali a lokacin mulkinsa, kuma ganin su da kansu sojojin da suka yi juyin mulkin sun ba da hujjojin da suka kai su ga yin wannan juyin mulki.

Jamhuriyar Nijar | Mahamadou Issoufou
Mahamadou Issoufou tsohon shugaban Jamhuriyar NijarHoto: Boureima Hama/AFP

A fuskar kungiyon da ke yaki da cin hanci da karbar rashawa da a baya suka mayar da wannan batu a matsayin tasu kokowa na ganin cewa shi fa batun yaki da cin hanci da almundahana da dukiyar kasa dole sai an bai wa gawa kashi mai rai zai soma jin tsoro. Sai dai daga bangaran kungiyar nan da ke fafutukar kare hakin dan Adam da shinfida dimukuradiyya ta SEDEL DH/Niger ta bakin shugabanta Alhaji Baba Al Makiyya abin da suke bukata shi ne tsohon shugaban Issoufou Mahamadou ya fuskanci shari'a domin ya wanke kansa su kuma 'yan kasa su san gaskiyar lamarin abin da ya faru kan zarge-zargen da ake yi masa.

Abun jira a gani shi ne ko wace amsa ce hukumomin na Jamhuriyar Nijar za su bayar kan wannan batu na tsohon shugaban kasar Issoufou Mahamadou wanda kuma har yanzu yake a matsayin shugaban wannan tsari na kasuwanci na bai daya na ZLECAF na Tarayyar Afirka wanda bulaguronsa kadai ke tayar da cece-kuce mai yawa a kasar.