1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Xi Jinping: China na iya amfani da karfi kan Taiwan

Abdullahi Tanko Bala
October 16, 2022

Shugaban kasar China Xi Jinping ya ce gwamnatinsa za ta cigaba da jan ragamar manufofi kan Hong Kong da Taiwan manyan batutuwa biyu da suka jefa ta cikin takun saka da Amirka da wasu kasashen duniya.

https://p.dw.com/p/4IG6v
Shugaban China Xi Jinping
Shugaban China Xi JinpingHoto: Thomas Peter/REUTERS

Shugaba Xi Jinping ya ce China za ta cigaba da aiwatar da manufofin na sha'anin mulki a kan Taiwan da kuma yankin Hong Kong mai kwarya kwaryar cin gashin kai inda gwamnatinsa ta kakaba dokar tsaro ta kasa a birnin Hong Kong da mahukuntan yankin suka yi dirar mikiya akan yan adawa da masu rajin cigaban dimukuradiyya. Matakin kuma da Amirka da wasu kasashe suka yi kakkausar suka akai.

Xi Jinping ya ce za su ci gaba da kokarin hade yankunan cikin kwanciyar hankali da kuma gaskiya da adalci sai dai ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen amfani da karfi idan bukatar hakan ta taso.

Wakilai a taron Jam'iyyar Kwamunisanci ta China karo na 20
Wakilai a taron Jam'iyyar Kwamunisanci ta China karo na 20Hoto: Huang Jingwen/Xinhua via AP/picture alliance

"Warware batun Taiwan magana ce ta kasar China kuma batu ne wanda ya zama wajibi a garemu, jama'ar China. Za mu ci gaba da kokarin hadin kai ta masalaha to amma ba za mu fidda tsammanin yin amfani da karfi ba, kuma muna da damar daukar dukkan matakin da muka ga ya ya zama wajibi. Wannan ya shafi masu yi mana katsalandan daga waje da kuma tsirarun yan aware da ke neman yancin kan Taiwan."

Su ma 'yan siyasa a yankin Hong da Macao sun baiyana fatan samun damammaki a yankunan biyu da za su daukaka yankunan da kuma sajewarsu don cigaban kasa. John Lee Ka-chiu shugaban yankin Macao yayi bayani yana mai cewa:-

"Gwamnatin tsakiya ta damu da halin da ake ciki a Hong Kong shi ya sa ta samar da dokar tsaro ta kasa baki daya kuma tuni ta inganta tsarin zabe a Hong Kong wanda muhimmin mataki ne na aiwatar da manufar kasa daya tafarki biyu a hukumance."

Yayin da yake jawabi game da manufofin China na harkokin kasashe waje, shugaban kasar Xi Jinping ya ce China har kullum tana da kudirin riko da wanzuwar zaman lafiya a duniya da dabbaka ayyukan cigaban al'umma. Ya yi kira ga kasashen duniya su riki akidar zaman lafiya don cigaban al'umma baki daya.

Shugaba Xi Jinping yayin gabatar da jawabi a taron Jam'iyyarsu
Shugaba Xi Jinping yayin gabatar da jawabi a taron Jam'iyyarsuHoto: Mark Schiefelbein/AP Photo/picture alliance

"China ta na nan kan kudirorinta na manufofin harkokin waje da tabbatar da dorewar zaman lafiya a duniya da bunkasa cigaban al'umma da samar musu kyakkyawar makoma a gaba bisa hadin kai da fahimtar juna." 

Shugaban ya kuma yi nuni da cewa Jam'iyarsu ta kwamunisanci ta China CPC ta cimma gagarumar nasara a cikin shekaru goma da suka gabata. 

"Shekaru goma da suka wuce an ga gagarumin cigaba a fannoni guda uku masu tasiri ga jam'iyya da kuma al'umma, yaki da annobar corona da cigaban tattalin arziki da kuma yaki da talauci. Mun aiwatar da cika shekaru 100 na kafuwar jam'yyar kwamunisanci da dabbaka sabon tsarin gurguzu da ya dace da akidar China".

A yayin taron jam'iyyar kwamunisancin ta China, ana sa rai shugaba Xi Jinping zai sami sahalewa ta yin tazarce wa'adi na uku a karagar mulki tare kuma da tsara ayyukan cigaban kasar na shekaru biyar masu zuwa.