1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Wutar zanga-zanga ta kunnu a kasar Yuganda

July 23, 2024

A Yuganda, an ja daga tsakanin matasa masu zanga-zangar adawa da cin hanci da rashawa da jami'an tsaro, boren da ya fara aiki daga wannan Talata. Shugaba Yoweri Museveni dai ya gargade su da cewa kada su yi wasa da wuta.

https://p.dw.com/p/4idbC
Wasu masu zanga-zanga a birnin Kampala
Wasu masu zanga-zanga a birnin KampalaHoto: AP Photo/picture alliance

Masu zanga-zangar dai na Yuganda sun ja daga, sun ce babu gudu ba ja da baya, zanga-zanga kama daga wannan Talata babu fashi. A yayin da gwmanati ke amfani da kafafen yada labarai da sauran hanyoyin wajen isar da sakon gargadi kan zanga-zangar, matasan na Uganda na amfani da shafukan sada zumunta wajen nuna turjiyarsu, inda suka lashi takobin yin jerin gwano zuwa majalisar dokoki, kamar matashiya Uweri Lyndah, wacce ta rubuta a shafinta na X cewa ta gaji da tsoron da ake bai wa matasan kasar, a wannan karon babu makawa sai sun fito. Lauyan da ke da kware kan kare hakkin dan Adam a kasar  Eron Kiiza ya shaida wa DW cewa cin hanci a gwamnati ne ke kara hassala matasa fitowa zanga-zanga

'Yancin fitowa zanga-zanga na nan kunshe a cikin kundin tsrain mulkinmu. Hakan bai rataya kan ra'ayin wani ko shugaban Uganda ba. A saboda haka mutanen da ke son zanga-zanga ta lumana, ba sa bukatar wani izini kuma ba za a iya hana su hakan ba. Mun fahimci ra'ayin shugaban kasa, amma ba ra'ayin doka ba ne.''

Karin bayani: Matsalar hana 'yancin fadin albarkacin baki

Tuni dai Shugaba Yoweri Museveni na Yuganda ya gargadi matasan masu shirin fitowa yi wa gwmanatinsa zanga-zanga da cewa su kiyayi wasa da wuta, furucin da ya razana wasu matasan kasar ya kuma jefa tsoro a zukatan masu zanga-zangar kamar yadda lauya Kiizo ya yi karin haske.

''Mutane za su tsorata, babu shakka, ana jin tsoron shugaban kasa, ana kuma jin tsoron 'yan sanda saboda tarihin abubuwan da suka yi a baya. Amma na san akwai gwarazan mutanen da kowace irin barazana aka yi musu sai sun fito sun yi zanga-zangar lumana.''

Rundunar 'yansanda Yuganda ita ma ta sake jaddada matsayarta a Litininin din nan da ta gabata, inda ta gargadi masu son fitowa zanga-zanga da su tsaya a gida. Sai dai masana na cewa shekara da shekaru na mulkin Yoweri Museveni mai kama da mulkin danniya, ya siffantu da rufe wa mutane baki, Oryem Nyeko, babban mai nazari kan hakkin dan Adam a Yuganda da Tanzaniya mahukunta a Kampala na toshe duk wata kofa da wani zai yi musu nasiha.

''Jama'a na samun damar kalubalantar gwmanati a kafofin yada labarai, amma akwia hanyoyi da dama da aka hana jama'a nuna rashin gamsuwarsu kan yadda ake tafiyar da kasarsu. Daya daga cikin hanyoyin da aka toshe ita ce zanga-zanga kamar yadda tarihi ya nuna yadda jam'an tsrao ke murkushe kusan duk wanda ya fito ya daga murya.''

Yunkurin zanga-zangar ta Yuganda dai ya samo tushe ne daga abin da ya faru a makwabciyar kasa, Kenya, inda zanga-zangar adawa da kara kudin haraji ta rikide zuwa zanga-zangar bukatar murabus din Shugaba William Ruto. Sai dai a Uganda kungiyoyin fararen hula sun ce tabargaza da kwasar dukiyar kasar da ke gudana su ne ke kara wa jama'a karfin gwiwar fitowa zanga-zanga da gwamnatin Yoweri Museveni da ya kwashe shekaru 38 kan karagar mulki.