1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wutar daji ta kashe mutane 50 a Girka

July 24, 2018

Sama da mutum 50 ne aka tabbatar da cewa sun mutu sakamakon wata gobarar daji a wajen birnin Athens na kasar Girka.

https://p.dw.com/p/31yVu
Griechenland | Waldbrände
Hoto: Reuters/C. Baltas

A cewar hukumomin kasar ta Girka, akwai ma wasu sama da 150 da ke kwance a asibiti cikin mummunar yanayi.

Cikin daren Talata ne dai wutar ta kama wani daji da ma wasu kauyukan da ke kewayen birnin na Athens, har i zuwa wayewar gari.

Masu aikin ceto sun ce suna kokarin taimaka wa wadanda ke bukatar dauki.

Wasu hotunan bidiyo sun nuno yadda wasu mazauna ke kokarin tserewa cikin motoci, yayin da wasu gidaje da saurarn gine-gine ke ci da wuta.

Tuni ma dai hukumomin yankin suka ayyana dokar ta-baci a wuraren da lamarin ya auku.