1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wuta ta lafa a Siriya

April 12, 2012

Sabanin yadda aka so tun da farko, a yau Alhamis an samu nasarar dakatar da bude wuta a kasar Siriya

https://p.dw.com/p/14bzG
In this image made from amateur video released by the Syrian Media Council and accessed Tuesday, April 10, 2012, smoke rises following purported shelling in Homs, Syria. Syrian troops shelled and raided opposition strongholds across Syria on Tuesday, activists said, denying claims by the foreign minister that regime forces have begun pulling out of some areas in compliance with a U.N.-brokered truce. (Foto:Syrian Media Council via AP video/AP/dapd) TV OUT, THE ASSOCIATED PRESS CANNOT INDEPENDENTLY VERIFY THE CONTENT, DATE, LOCATION OR AUTHENTICITY OF THIS MATERIAL
Hoto: dapd

An kaddamar da matakin tsagaita wutar da aka dade ana jira a gani a Siriya ranar Alhamis, ba tare da an sami rahotannin tashe-tashen hankula ba daga karfe shidda na safe. Gwamnatin Siriya ta yi alkawarin ba da hadin kanta ga matakin tsagaita wutar da manzo na musamman na sassanta rikicin, Kofi Anan ya bayar a yayin da ta nemi 'yancin kare kanta daga duk wani hari da 'yan tawaye za su yi yunkurin kai mata. Gwamnati a Damascus bata cika wa'adin farko na ranar Talata wanda ya tanadi da ta janye dakarunta daga wurare masu yawan al'umma ba.

Wannan rikicin na Siriya ne ya fito kan gaba a taron kasashe masu manyan masana'antu na G8 wanda ya wakana a birnin Washington ranar Laraba, inda Birtaniya ta bukaci kasashen da su kara mara wa 'yan adawa baya, idan har Damascus ta gaza cika alkawarinta. Faransa a waje guda kuma, ta yi kira ga masu sanya ido na Majalisar Dinkin Duniya da su kula da yadda ake aiwatar da tanadin yarjejeniyar tsagaita wutar. Bisa bayanan wata sanarwar da Fadar white House ta fitar, shugaba Barack Obama da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel sun amince lokacin wani zantawarsu ta wayar tarho da su bukaci Kwamitin Sulhu ya dauki mataki mai tsauri kan Bashar al-Assad saboda rashin amincewarsa da shirin sulhun a kan kari.

Mawallafiya: Pinado Abdu-Waba
Edita: Halima Balaraba Abbas