1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

W.H.O. ta yi gargadi kan karuwar annobar corona

June 20, 2020

Hukumar Lafiya ta Duniya ta yi gargadi kan yiwuwar sake ganin sabon babi mai hadari dangane da annobar corona a duniya daidai lokacin ke bazuwa a yankunan Amirka.

https://p.dw.com/p/3e4a8
Tedros Adhanom Ghebreyesus
Hoto: Getty Images/Afp/F. Coffrini

 

Hukumar ta lafiya a duniyar na wannan gargadin ne a ranar Jumma'a, yayin da wadanda cutar corona ta kama a kasar Brazil kadai a yanzu suka haura mutum miliyan guda. Kasashen Colombia da Mexico ma dai lamarin ya kazanta, inda suke da sama da mutum dubu 20 kowannensu da cutar ta kashe.

Sai dai a nahiyar Turai, hukumomi na sassauta matakai ne da suka shafi hana yaduwar annobar, musamman dokar kulle saboda fargabar tabarbarewar harkokin tattalin arziki. Kasar Amirka wacce ta fi kowacce yawan wadanda cutar ta kama, a yanzu wadanda ta kashe sun zarta mutum dubu 119, daidai lokacin da Shugaba Trump ke fama da yakin neman zabe karo na biyu.