1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

WHO ta soki kasashen da ke siye rigakafin corona

January 19, 2021

Babban daraktan Hukumar Lafiya ta Duniya Tedros Adhanom Ghebreyesus ya soki kasashe masu arziki da ke siyewa da kuma rubda-ciki a kan allurar rigakafin corona.

https://p.dw.com/p/3o80m
Brasilien Corona-Pandemie | Impfstart | CoronaVac Sao Paulo
Hoto: Nelson Almeida/AFP

Tedros Adhanom Ghebreyesus ya yi gargadin cewa rashin rarraba allurar rigakafin coronavirus ga kasashe masu fama da talauci da kasashe masu arziki ke yi ka iya tsawaita lokacin annobar, inda ya soki kasashen masu arziki da siyewa da kuma tara rigakafin da ake da su a halin yanzu.

Kazalika ya kuma ce kasashe masu arziki za su kasance cikin hadari idan har suka yi biris da kasashe masu fama da talauci.

Ghebreyesus, ya ce a halin yanzu shirye-shiryen fara isar da allurar rigakafin cutar a watan Fabrairu ga yawancin kasashen da ke fama da talauci a duniya na fuskantar kalubale.

A makon da ya gabata dai jami'ar Johns Hopkins ta ce mutanen da suka mutu sanadiyar annobar sun haura mutum miliyan biyau a duniya.