1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

WHO ta damu da karuwar corona a Turai

August 30, 2021

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta baiyana damuwa kan yadda cutar Corona ke dada karuwa a nahiyar Turai.

https://p.dw.com/p/3zhmt
ITALY-CHINA-HEALTH-VIRUS
Hoto: Alberto Pizzoli/AFP/Getty Images

A makon da ya gabata an sami karuwar kashi 11 cikin dari na mace-mace a yankin inda wasu alkaluma ke cewa ana tsammanin za a sami mutum 236, 000 da za su rasu zuwa daya ga watan Disambar wannan shekarar a cewar darakta mai kula da nahiyar turai a hukumar lafiyar ta duniya Hans Kluge kamar yadda ya shaidawa manema labarai a Copenhagen.

Kawo yanzu mutum miliyan daya da dubu dari uku suka rasu a sakamakon cutar Corona a nahiyar Turai tun bayan barkewar annobar.