1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

WHO: Sauro ya zama annoba a Burundi

August 20, 2019

Miliyoyin mutane ne aka tabbatar da cewa sun kamu da zazzabi a bana kadai, yayin da wasu daruruwan ma suka mutu a Burundi. Amma hukumomi, sun ce babu annobar da ta kama da haka a kasar.

https://p.dw.com/p/3ODgz
Symbolbild Malaria
Hoto: picture-alliance/dpa

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, ta ce kimanin mutum miliyan shida daga cikin miliyan 11 da ke kasar Burundi sun kamu cutar zazzabin cizon sauro wato Maleriya.

Wani rahoton da hukumar ta fitar ne ya tabbatar da zazzabin a Burundi, inda ta ce an tattara bayanai ne daga watan Janairu zuwa watan jiya wato Yuli.

Hukumar ta lafiya a duniya, ta kuma ce akwai kamar mutum dubu da dari takwas da sittin da zazzabin ya halaka.

To sai dai fa ma'aikatar lafiya a Burundin, ta musanta bullar wata annoba a kasar.