1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

WHO: Kwararrun sun isa cibiyar binciken Wuhan

February 3, 2021

Masu bincike na hukumar Lafiya ta Duniya WHO sun ziyarci Cibiyar binciken kwayoyin cututtuka masu yaduwa ta Wuhan da ke China.

https://p.dw.com/p/3onnX
China | Coronavirus | WHO Experten in Wuhan | Jinyintan Hospital
Hoto: Hector RetamalAFP/Getty Images

Kwararrun na ci-gaba da kokarin na neman amsoshi kan asalin cutar coronavirus. An sha hasashen cewa an sami farkon bullar cutar ne daga cibiyar binciken kwayoyin cututtuka ta Wuhan din, sai dai yawancin masana kimiyya sun ki yarda yayin da wasu ke hasashen an yi kwajin kwayar cutar ne wanda asalinta daga dabba aka samu a cibiyar kafin bullarta ta hanyar guda daga cikin ma'aikatan.

Masu binciken Hukumar Lafiya ta Duniya dai ba su fitar da kowani sakamako ba sai dai jagoran tawagar kwararrun jami'an Peter Ben Embarek ya ce zai tabbatar da ya gana da dukan wadanda suka dace ya kuma yi musu tambayoyi masu mahimmanci.