1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cutar Marburg mai hatsari ta sake bazuwa a Ghana

July 27, 2022

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce kawo yanzu mutum 180 take hasashen sun yi cudanya da masu cutar ta Marburg a Ghana, kuma hukumomi na kokarin ganin sun gano su an killace su.

https://p.dw.com/p/4Ek6O
ECOWAS Westafrikanische Staaten verhängen Sanktionen gegen Mali und Guinea
Hoto: Nipah Dennis/AFP

Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, ta tabbatar da samun karin mutum biyu dauke da cutar Marburg a kudancin kasar Ghana. Wani babban jami'in WHO a kasar Ibrahima Soce Fall ne ya sanar wa da 'yan jarida haka a Larabar nan, makonni biyu bayan da aka fara sanar da bullar cutar mai hatsari kamar na Ebola a kasar. 

Da ma dai akwai mutane biyu da WHO din ta ce cutar ta halaka a yankin Ashanti bayan sun nuna manyan alamun kamuwa da cutar da suka hada da; gudawa da zazzabi mai zafi da kuma amai. 

Masana dai na cewa jemage ne ke yada wa dan Adam wannan ciwo da akan iya baza shi ta hanyar taba ruwan jikin wanda ya kamu da shi.