1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

COVID-19: Ya kamata a koma makaranta

Rémy Mallet GAT/LMJ
August 21, 2020

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO da Asusun Kula da Ilimin Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya, sun yi kira ga kasashen Afirka da su gaggauta bude makarantun boko da aka rufe da nufin dakile yaduwar annobar COVID-19.

https://p.dw.com/p/3hIkE
Burundi Schule in Bujumbura
Ya kamata yara su koma makarantu a Afirka in ji WHO da UNICEFHoto: picture-alliance/dpa/T. Schulze

Cikin wata sanarwar hadin gwiwa daHukumar Lafiyar ta Duniya WHO da Asusun Kula da Ilimin Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniyar din suka fitar, sun nunar d acewa ya kamata a bai wa yaran damar ci gaba da karatunsu. Sai dai kuma sun bukaci kasashen da su tabbatar sun tanadi matakan kariya a makarantun. Makarantun bokon dai, sun kasance a rufe tsawon watanni hudu zuwa shida da suka gabata.

A Najeriya ga misali, tun cikin watan Maris din wannan shekarar ne aka rufe makarantun, lamarin da ya sanya daruruwan daliban jami'o'i gudanar da wani taro a ranar Larabar da ta gabata a birnin Abuja, inda suka yi kira da a bude makarantun. Kasar kenya daga nata bangare ta dauki matakin rufe makarantun ne baki daya har sai shekarar badi. Ana dai ganin wadannan matakan na yin illa ga tattalin arzikin kasashen da ma makomar yara. Hukumar ta WHO ko OMS ta ce dadewar yara ba tare da zuwa makaranta ba, na tattare da hadari ganin da dama daga ciki sun kasa komawa makarantar baki daya.

Kenia I Coronavirus
​​​​Yara a Kenya na gararanbaHoto: picture-alliance/AP Photo/File/B. Inganga

Akan haka ne ta yi kira da a gaggauta bude makarantun kamar dai yadda Matshidiso Moeti daraktan hukumar ta WHO a Afirka ya yi karin haske: "Wani hasashen da Babban Bankin Duniya ya yi, na nuni da cewa rufe makarantu da aka yi a kasashen Kudu da Sahara na iya haddasa asarar dalar Amirka dubu hudu na kudin shiga a shekaru masu zuwa ga kowane yaro daya. Kuma ba za mu taba bari hakan ya auku ba. Dan haka muke bukatar da a bude makarantun. Amma kuma ya kamata a dauki matakin saka tazara tsakanin dalibai a cikin makarantun tare da samar wa dalibai takunkuman kariya da ruwa domin tsaftace hannuwansu."

Hukumar Lafiya ta Duniyar reshen Afirka ta ce akalla yara miliyan 18 ne ke samun abinci a makarantu a kasashen na Kudu da Saharar Afirka, kuma ci gaba da zaman yaran a gida na iya haddasa matsalar karancin abinci ga iyalai da dama a Afirkan, wadanda dama suna fama da matsalar rashi da kangin talauci. A nasa bangare Asusun Kula da Ilimin Kananan Yaran na UNICEF, ya ce ko baya ga matsalar karancin abinci yaran da ba sa zuwa makaranta na cikin hadarin fuskantar kuntatawa da cin zarafi a lokacin zaman gida.

Malawai Salima | Schuelerinnen und Schueler der Kalani-Schule
Matsalar karancin abinciHoto: Imago Images/epd/S. Vogt

Sai dai Mohamed Malick Fall daraktan hukumar ta UNICEF a yankin gabashi da kuma kudancin Afirka, ya ce matsawar gwamnatoci ba su saka hannu a aljihu ba wajen samar da matakan kariya ga komawa makarantar, to abin zai yi wuya. Asusun na UNICEF ya ce yara sama da miliyan 140 ne suka daina zuwa makaranta a Afirkan, tun bayan matakin kullen da kasashen suka dauka da nufin dakile yaduwar annobar cutar corona.

Sai dai Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce daga nasu bangare kasashen Turai ba sa bukatar sake daukar matakan kulle a kasashensu, duk da yadda sannu a hankali cutar ke kara yaduwa a wasu kasashen kamar Jamus da  Faransa da Italiya da Spain, tana mai cewa matakan da kasashen Turan suka dauka wajen tunkarar cutar da kuma darasin da suka samu a game da ita, za su iya taimaka musu ga kawar da fargabar da ake da ita ta sake farfadowar annobar a zagaye na biyu, wacce ya zuwa Juma'a wannan makon ta kama mutane sama da da miliyan 22 da dubu 500 a fadin duniya, tare da halaka wasu mutane kusan dubu 80 a yayin da wasu sama da miliyan 14 da dubu 500 suka warke.